BBC Hausa
today at 04:49. Facebook
Lucas Leiva ya ci kwallonsa ta farko a Liverpool cikin shekara 7, wadda ta ba su damar zuwa zagaye na hudu na gasar cin kofin FA a karawarsu da kungiyar Plymouth da ke gasar League Two. Me za ku ce?

Kofin FA: Liverpool ta doke Plymouth 1-0 - BBC Hausa

bbc.com
BBC Hausa
today at 04:34. Facebook
Yau ne wa'adin shugaban Gambia na sauka daga mulkin kasar ya kare amma kuma yaki sauka. Sannan sojoji daga Najeriya da Senegal suna zaman jiran ko-ta-kwana. Shin ko me ya sa Jammeh kin sauka daga mulki?

Me ya sa Jammeh ba ya son sauka daga mulki? - BBC Hausa

bbc.com
BBC Hausa
today at 04:30. Facebook
Masu sauraro, ga wannan bidiyo domin ba ku damar sanin kadan daga cikin abubuwan da shirinmu na safe ya kunsa. Ka da ku manta za ku iya tafka mahawara kan batutuwan. Da fatan za ku kasance da sashen Hausa na BBC.
BBC Hausa
today at 03:41. Facebook
Shugaban Amurka mai barin gado, Barack Obama ya gargadi magajinsa, Donald Trump da ya kula wajen sake kulla alaka da Rasha. Mene ne ra'ayinku?

Obama ya gargadi Trump kan cire wa Russia takunkumi - BBC Hausa

bbc.com
BBC Hausa
yesterday at 20:37. Facebook
Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce mutum tara kawai aka kai zuwa Maiduguri don samun cikakkiyar kulawa bayan harin kuskure da sojin sama suka kai kan fararen hula. Me ya kamata a yi wa wadanda lamarin ya shafa?

Nigeria: A gaggauta taimaka wa mutanen da harin soja ya jikkata

bbc.in
BBC Hausa
yesterday at 19:53. Facebook
Rundunar sojin sama ta Najeriya ta tura sojoji 200 zuwa Senegal domin karfafa rundunar kasashen Ecowas da ke shirin kawar da Shugaba Yahya Jammeh na Gambia da karfin tuwo. Ko wannan mataki ya dace?

Nigeria ta tura sojoji 200 da jiragen yaki don kawar da Jammeh

bbc.in
BBC Hausa
yesterday at 18:23. Facebook
Harin da wani jirgin yakin Najeriya ya kai kan wani sansanin 'yan gudun hijira bisa 'kuskure' da ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 70, ya sa mun yi nazari kan wasu hare-hare irin wannan da aka kai a wasu kasashen duniya.

Kun san hare-haren da soji suka kai bisa kuskure? - BBC Hausa

bbc.in
BBC Hausa
yesterday at 17:24. Facebook
Wasu masu sharhi kan siyasar Amurka sun ce 'yan Afirka sun fi cin moriyar tsohon shugaban Amurka, George Bush fiye da Obama. Kun yarda da haka ko kuna da ja?

''Yan Afirka sun fi morar Bush a kan Obama'

bbc.in
BBC Hausa
yesterday at 16:59. Facebook
Kungiyar Everton ta ki amincewa da tayin da AC Milan ta bukaci a ba ta aron Gerard Deulofeu domin ya buga mata tamaula zuwa karshen wasannin bana.

Everton ta ki bai wa Milan aron Deulofeu

bbc.in
BBC Hausa
yesterday at 16:30. Facebook
Watakila dan wasan Manchester United Memphis Depay, ya koma taka-leda a kungiyar Lyon ta Faransa a cikin watan Janairu.

Watakila Memphis Depay ya koma Lyon

bbc.in
BBC Hausa
yesterday at 16:12. Facebook
Tun bayan da Donald Trump ya ci zaben shugaban Amurka, sai fargaba ta fara shiga zukatan ma fi yawan 'yan Afirka kan irin salon mulkin da zai gudanar da ka iya mayar da su saniyar ware. Shin ko me ya sa hakan? Za ku ji sharhi cikin wannan labari.

Me ya sa shugabannin Afirka ke tsoron mulkin Trump?

bbc.in
BBC Hausa
yesterday at 16:01. Facebook
Real Madrid za ta karbi bakuncin Celta de Vigo a wasan farko a Copa del Rey a karawar daf da na kusa da karshe.

Madrid za ta karbi bakuncin Celta a Copa del Rey

bbc.in
BBC Hausa
yesterday at 14:22. Facebook
Kun san hare-haren da soji suka kai bisa kuskure? Harin da wani jirgin yakin Najeriya ya kai kan wani sansanin 'yan gudun hijira bisa 'kuskure' da ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 70, ya sa mun yi nazari kan wasu hare-hare irin wannan da aka kai a wasu kasashen duniya.

Kun san hare-haren da soji suka kai bisa kuskure?

bbc.in
BBC Hausa
yesterday at 13:53. Facebook
Ko kun san dabbar da ta fi yawan hayayyafa a duniya [ Bbc.in Link ]

Ko kun san dabbar da ta fi yawan hayayyafa a duniya

bbc.in
BBC Hausa
yesterday at 13:30. Facebook
Shin a ganinku me ya sa Yahaya Jammeh ba ya son barin gadon mulki? Kuna iya shiga ku karanta labarin domin jin dalilan da masu sharhi suka bayar.

Majalisar Gambia ta tsawaita wa'adin Yahya Jammeh

bbc.in
BBC Hausa
yesterday at 12:16. Facebook
Rundunar sojin Nigeria na ci gaba da nuna alhininta kan 'kuskuren' da ta yi na jefa bam a wani sansani na 'yan gudun hijira, da zaton cewa wajen taruwar mayakan Boko Haram ne.

Mun yi da-na-sanin kai hari kan farar hula — Sojoji

bbc.in
BBC Hausa
yesterday at 10:26. Facebook
Hukumomi a Masar sun sanya sunan tsohon fitaccen dan kwallon kafar kasar Mohamed Aboutrika a cikin jerin 'yan ta'dda saboda alakarsa da kungiyar 'Yan Uwa Musulmi. Kuna ganin hakan ya dace kuwa?

Masar ta sanya tsohon dan kwallo Mohamed Aboutrika cikin 'yan ta'adda

bbc.in
BBC Hausa
yesterday at 09:25. Facebook
Dubban 'yan kasar Birtaniyan da kamfanin yawon bude ido na Thomas Cook ke mu'amala da su na fice wa daga Gambia suna komawa kasarsu bayan ma'aikatar kasashen waje ta ba su shawarar yin hakan sakamakon tsoron barkewar rikici. Yaya kuka ga matakin?

Tsoron barkewar rikici ya sa 'yan yawon bude ido na tsere wa daga Gambia

bbc.in
BBC Hausa
yesterday at 07:02. Facebook
Wata mata Summer Zervos, da ta zargi shugaban Amurka mai jiran gado, Donald Trump, da sumbatarta tare da taba mata jiki, ta kai kararsa kotu bisa keta mata mutunci saboda karyata zargin nata da ya yi. Ya kuke ganin lamarin?

Zargin lalata: An kai karar Donald Trump kotu - BBC Hausa

bbc.com
BBC Hausa
yesterday at 06:29. Facebook
Shugaba Barrack Obama ya zaftare hukuncin zaman gidan yari na shekara 35 da aka yanke wa wata mata sojar kasar, saboda bayar da bayanan sirrin kasar da ta yi, wanda ya fi kowanne muni a Amurka. Me za ku ce?

Wikileaks: Obama ya yi wa Chelsea Manning afuwa - BBC Hausa

bbc.com